Thailand na fama da hare-haren bama-bamai


Akalla mutane hudu sun rasu a kasar Thailand, sakamakon jerin hare-hare da yammacin ranar Alhamis da kuma safiyar wannan Juma’a a birnin Hua Hin.

 0,,19469432_303,00 (2)

Babban darektan ‘yan sandan birnin na Hua Hin Janar Sithichai Srisopacharoenrath, ya ce bama-bamai biyu an boye su ne cikin wasu shuke-shuke a wani titi mai cinkoson jama’a inda masu yawon buda ido ke halarta, kuma jami’an tsaro da suka danganta lamarin da wani shiri na neman tada zaune tsaye a kasar, sun ce su na kokarin gano wadanda ke da alhakin kai wadan nan hare-hare.

Akalla kuma mutane 21 sun sami raunuka, cikinsu har da baki ‘yan yawon bude ido da suka hada da ‘yan kasar Netherlands, Italiya da kuma Jamus.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like