Theresa May ta nada sabbin ministoci


Sabuwar Firai Ministar Birtaniya Theresa May ta yi manyan nade nade a gwamnatin ta inda ta bayyana Boris Johnson, jigo a fafutikar ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar turai a matsayin ministan harkokin waje.

Mr Johnson, wanda shi ne tsohon magajin garin birnin London ya ce yanzu Burtaniya na da damammaki na inganta dangantakarta da nahiyar turai da kuma sauran kasashen duniya.

A jawabinta na farko jim kadan bayan kama aiki, Mrs May ta yi gargadin cewa yanzu an shiga wani yanayi ne na gagarumin sauyi a kasar.

Sai dai ta yi alkawarin cewa kasar zata samar wa kanta sabuwar alkibla.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like