
Zaɓabben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa ya gana da babban jojin Najeriya a birnin London na ƙasar Ingila.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ta bayyana labarin a matsayin ƙage maras tushe.
A cikin kwanakin nan ne wasu jaridu da kuma masu amfani da shafukan sada zumunta suka rinka yaɗa labarin yadda aka yi wata ganawar sirri, tsakanin Bola Ahmed Tinubu da babban jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola.
Labarin ya nuna cewa babban jojin ya yi ɓadda-bami ta hanyar hawa keken guragu domin ganawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a birnin London.
Sai dai sanarwar, wadda aka fitar ta ce an ƙirƙiri labarin ne domin sanya shakku a zukatan ƴan Najeriya game da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen da ya gabata.
Sanarwar ta ce “muna musanta wannan labari na ganawa tsakanin zaɓabben shugaban ƙasa da babban jojin Najeriaya, da ƙaƙƙrfar murya.”
A cikin sanarwar, Mr Onanuga ya ce yanzu haka Bola Tinubu, wanda ya bar Najeriya a ranar Talatar da ta gabata , yana a ƙasar Faransa, inda yake hutawa domin sauke gajiyar yaƙin neman zaɓe.
Sai dai ya ce Tinubun zai isa birnin London ne nan gaba, kafin ya tafi Saudiyya domin yin Umara.
A cikin watan Fabarairu ne Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya inda ya samu galaba a kan Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour.
Atiku da Obi sun garzaya kotu
Jam’iyyun adawa hudu a Najeriya sun shigar da ƙara domin ƙalubalantar nasarar zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Dan Takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubkar da na LP Peter Obi da na AA Solomon Okangbuan da kuma na jam’iyyar APM Chichi Ojei duka sun shigar da ƙara gaban kotun ƙorafin zaɓe domin ƙalubalantar nasar Tinubu sa’o’i kafin cikar wa’adin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama na ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Manyan ‘yan takarar hamayyar biyu Atiku Abubakar da Peter Obi sun nemi kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen da ta ayyana cewa Tinubu bai ci zaɓen da aka gudanar ba.
Peter Obi ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuri’u a jihohin Rivers da Legas da Taraba da Benue da Adamawa da Imo da Bauchi da Borno da Kaduna da kuma jihar Plateau.
Obi na buƙatar kotun da ta ƙwace takardar shaidar cin zaɓe da hukumar INEC ta ba shi, tare da ba shi sabuwar takardar shaidar cin zaɓe.
Ranar Talata da yamma ne Amurka ta fitar da wata sanarwa tana mai Allah wadai da ƙaruwar razanar da masu kaɗa ƙuri’a da sauran laifukan zaɓe da ta ce an aikata a lokacin zaɓen gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris.