
Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyar APC ya dawo gida Najeriya a jiya Lahadi daga kasar Saudiya inda yayi aikin Umrah.
Tinubu ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubarkar na daga cikin mutanen da suka tarbe shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.


