Tinubu Ya Gana Da Kungiyoyin Malaman Musulmi Na Yankin Arewa Maso Yammacin NajeriyaYayin ganawar, ya yi alkawari cewa, zai kafa hukuma ta musamman da zata magance matsalolin almajirai a lardin arewacin Najeriya.

Malamai daga dariku daban daban ne da kuma kungiyoyin musulinci a dukkanin jihohi 7 na shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ne suka hallara a Kano domin saurarar jawabi mai kunshe da alkawura daga bakin dantakarar shugaban kasar na APC Bola Ahmed Tinubu.

A yayin jawabin, dantakarar na APC ya yi alkawarin kafa hukuma ta musamman da zata kula da al’amuran da suka shafi matsalolin almajirai a yankin arewacin Najeriya. Yana mai cewa, muddin aka zabe shi ya yi alkawarin zai aiki kafada da kafada da malaman addinin musulinci domin lalubo hanyoyin kawo karshen matsalar almajirai a arewa. Baya ga haka Bola Tinubu ya yi alkawarin farfado da masana’antu a arewa, musamman a birni da kewayen Kano.

Tinubu Ya Gana Da Malaman Kungiyoyin Musulmi Na Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya

Tinubu Ya Gana Da Malaman Kungiyoyin Musulmi Na Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya

Gwamnan jigawa Badaru Abubakar dake zaman daraktan kwamitin tallata manufofin Bola Tinubu a yankin arewacin Najeriya ya musanta furicin da wasu keyi cewa, idan Tinubu ya ci zabe za’a kafa gwamnatin mutanen Lagos kawai. Yana mai cewa, ‘yan arewa dake kusa da Tinubu, kamar Malam Nuhu Ribado da gwamnan Kano da ma shi kan sa ba zasu bari aci amanar arewa ba, ko kuma a ci amanar musulinci.

Rawar da malamai ka iya takawa a fagen siyasa da shugabanci, shine batun da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi tsokaci akai, inda ya ce malamai nada muhimiyyar rawar takawa a wannan fage, kuma bada gudunmawa a siyasa ko shugabanci ba sai kana rike da katin Jam’iyyar siyasa.

Wakilai da shugabannin dariku da kungiyoyin musulinci a jihohi 7 na shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ne suka gabatar da jawabai a yayin ganawar dake zama wani banagare na tallata manufofin Bola Tinubu ga ‘yan Arewa gabanin babban zabe da za’ayi a watan gobe.

Saurari rahoton a sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like