Tinubu Ya Musanta Ganawa Da Gwamnoni 5 Da Suka Yi Wa PDP Tawaye A London
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Tunde Rahman, wanda ya ce wasu ne kawai suka kirkiro labarin don cimma muradinsu na siyasa.

Ko da yake Rahman ya kara da cewa duk da haka Tinubu na da ‘yancin ganawa da duk wani gwamna ko kungiyar da ya yi muradi don bunkasa siyasar sa.

Rahotanni sun bayyana cewa shi kansa madugun gwamnonin 5 wato gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa sun gana da Tinubu a lokacin da ya dawo Najeriya daga London.

Dan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo, wanda shi ma ya na London a lokacin, ya ce in Allah ya yarda nan ba da dadewa ba wadannan gwamnonin zasu fito su nanata goyon bayansu ga dan takararsu na jam’iyyar PDP.

Jigajigan jam’iyyar PDP irinsu tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa, na cewa aikin baban giwa ne ga gwamnonin tun da suna takarar mukamai a inuwar jam’iyyar.

Alamu na nuna PDP na shirin sa kafar wando daya da gwamnonin da ke ci gaba da daukar matakan angulu da kan zabo ga jam’iyyar.

Saurari rahoton cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like