Tinubu Ya Nada Sabbin Ministoci
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Jamila Bio Ibrahim daga Jihar Kwara a matsayin ministar matasa.

Kazalika ya nada Mista Ayodele Olawande daga jihar Ondo a matsayin karamin ministan matasa.

Nade-nade za su tabbata ne bayan Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ministocin biyu, wadanda za su jagoranci ma’aikatar kula da sha’anin matasa.

Dokta Jamila Bio Ibrahim, matashiyar likita ce kuma a baya-bayan nan ta rike mukamin Shugabar kungiyar Mata matasa ta PYWF.

Ta kuma yi aiki a matsayin babbar mataimakiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazak kan Manufofin SDGs.

Mista Ayodele Olawande kwararre ne a fannin ci gaban al’umma kuma daga cikin jagororin matasa a jam’iyyar APC.

Ya yi aiki a ofishin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kirkire-kirkire daga 2019 zuwa 2023.

Shugaba Tinubu ya bukaci matasan biyu da aka nada da su tabbatar da cewa sun nuna kwazo, kishin kasa, da kuma jajircewa wajen aiwatar da manufofi masu kyau na ilahirin matasan Najeriya.

~ Yusuf Aminu YusufSource link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like