Tsohon Gwamnan Legas kuma jigo a APC ya roki wasu manyan jam’iyyar wadanda ake hasashen suna shirin ficewa daga jam’iyyar wanda ya hada da Shugaban majalisar Dattawa, Saraki da Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso.
Shugaba Buhari ne dai ya nada Tinubu a matsayin Shugaban kwamitin da zai sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar da ke rigima da juna a matakin tarayya da kuma jihohi inda tsohon Gwamnan ya fara kai ziyara Sokoto inda ya sadu da Gwamna Tambuwal da kuma tsohon Gwamnan jihar, Wamakko.