Tsohon Gwamnan Legas kuma jigo a APC, Bola Ahmed Tinubu ya zargi Shugaban jam’iyyar na Kasa, John Odigie-Oyegun da gurgunta shirin sulhunta ‘ya’yan APC da ke rigima da juna tun daga matakin tarayya zuwa jihohi.
A cikin wata takarda da Tinubu ya rubutawa Buhari da shugabannin majalisar tarayya ya nuna cewa don cimma wata bukatar kansa,Shugaban APC na ci gaba da shirya makarkashiya na dakile wannan yunkuri na hada kan ‘ya’yan jam’iyyar. Kwanan nan ne dai, Buhari ya nada Tinubu a matsayin Shugaban kwamitin da zai sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar APC.