Ana sa ran Bola Ahmad Tinubu, jagoran jam’iyar APC,zai jagoranci wata tawagar manyan ƴan jam’iyar zuwa Dauran jihar Katsina inda za su gana da shugaban kasa Muhammad Buhari.
A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya jiga-jigan jam’iyar ta APC za su hallara a Daura domin yi wa shugaban ƙasar ta’aziyar mutane biyu da suka rasu a danginsa.
Tinubu da Bisi Akande sun gana da Buhari a ranar 13 ga watan Faburairu a fadar shugaban kasa dake Abuja.
A yayin ziyarar da suka kai masa Akande yace basun kai ziyarar bane dan tattauna batun siyasa ba, sun je ne domin yiwa shugaban gaisuwar ta’aziyar rashi da aka yi masa.
A cewar wata majiya ziyarar ta ranar Asabar ta wuce gaisuwar mutuwa kaɗai akwai batutuwa da dama da za su tattauna ciki har da batun sake tsayawa takarar shugaban a shekarar 2019.
A ranar juma’a ne shugaba Buhari ya karɓi baƙuncin gwamnonin jam’iyar APC a Daura.