Tirka-Tirka A Filin Jirgin Sama Na Abuja Sakamakon Kin Tashin Jirage


 nnamdi-azikiwe

Hargitsi da hayaniya sn kauraye filin jirgin sama naNmandi Azikiwe sakamakon soke tashin jirage ko kuma sauya lokutan tashinsu da kafatanin kamfaninnikan jiragen sama suka yi a yau din nan.

Rahoton da ya ke ishe na nuna cewa har zuwa karfe 12:40 na yau Laraba babu wani jirgi da ya sauka ko ya tashi daga filin jirgin saman na Abuja.

Wannan dalili ya sanya daruruwan fasijoji cikin damuwa tare da nuna rashin jin dadinsu cikin bacin rai.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto babu wani ma’aikacin hukumar kula da sauka da tashin jiragen sama ta kasa da ya yi wa fasinjojin bayanin dalilin kin tashin jiragen ko kuma tsaikon da aka samu.

Mun dai ga wasu fasinjojin suna ta barin filin jirgin yayin da wasu kuma suka dakata don ganin yadda za ta kaya.

Sai dai binciken ya nuna cewa rashin tashin jiragen na da alaka da karancin man jirgin sama da ake fama da shi a kasa.

A cikin sati biyun da suka gabata ma dai kamfanin jiragen First Nation da na Aero Contractors sun dakatar da aiki, inda a jiya kuma kamfani mafi girma na jirgin sama na Nijeriya, Arik Air su ma suka bayyana dakatar da zirga-zirga kafin daga baya su bayyana dawowa a yau.

Zuwa yanzu dai babu kamfanin jirgin sama da ya ke zirga-zirga

You may also like