
Asalin hoton, Real Madrid FC
Ranar Asabar Real Madrid ta lashe Fifa Club World, bayan doke Al Hilal 5-3 a Morocco.
Tono Kroos yana cikin ‘yan wasan da suka buga mata karawar, wanda ya dauki kofi na shida na zakarun nahiyoyin duniya.
Ya fara daukar daya a lokacin da yake Bayern Munich, yanzu ya ci na biyar tare da Real Madrid, wadda ta lashe na takwas jimilla.
Wasu ‘yan wasan Real Madrid da suka dauki Club World Cup biyar a kungiyar sun hada da Benzema da Nacho da Carvajal da kuma Modric.
Kofi na biyu kenan da Real ta lashe a kakar nan, bayan Uefa Super Cup.
Real wadda take ta biyu a bana a teburin La Liga da tazarar maki takwas ta yi rashin nasara a Spanish Super Cup a watan Janairu a hannun Barcelona a Saudia Arabia.
Real ta kai wasan karshe a Club World Cup, bayan cin Al Ahly 4-1 ranar Laraba, ita kuwa Al Hilal nasara ta yi a kan Flamengo 3-2 ranar Talata.
Real Madrid ita ce ke rike Champions League a Turai, ita kuwa Al Hilal ta Saudi Arabia ita ta lashe na zakarun Asia.