Tosho Dan Shekara 82 Da Aka Kama Da Kawunan Mutane Uku A Jihar Osun Ganiyu Oladosu an dai Kama shine a yankin Gbongan a jihar Osun bisa zargin mallakar kawuna da kuma sauran sassan jikin bil-adama.

Adetoyese Oyeniyi,basaraken gargajiyar garin dake karamar hukumar Ayedaade ta jihar Osun ya shawarci yan sanda da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da an hukunta mutumin da ake zargi. 

Oyeniyi yace Oladosu ya jawo abin kunya kan al’ummar yankin inda ya rantse cewa al’ummar garin baza su sake amimcewa da mutumin da ake zargin ba. 

Oladosu basarake ne da yafito daga gidan sarautar  Sooko dake garin. 

An dai Kama shine a gidansa dake dake Idifa,  a garin Gbongan. Inda daganan aka kaishi sashin kula da manyan laifuka na rundunar yan sandan jihar dake Osogbo.  

“Gbongan garine mai zaman lafiya abin tashin hankali da yafaru da Ganiyu Oladosu dan gidan Sarautar Sooko wanda aka kama da kawunan mutane  abune marar dadi da ya saba da al’adarmu, ” yace. 

Basaraken yayi kira da gwamnatin jiha da kuma rundunar yansandan jihar da su daukin batun da muhimancin gaske.

A kwanakin bayane dai mu kawo muku rahoton yadda mutanen garin na Gbongan suka jiwo wari na fitowa daga gidan mutumin bayan sun gudanar da bincike suka gano kawunan mutane da suka fara rubewa da kuma wasu sassan jikin dan adam. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like