
Asalin hoton, Getty Images
Tottenham na cikin kulob kulob din da ke zawarcin dan wasan Leicester City mai buga wa Ingila tsakiya James Maddison, 26. (Mirror)
Spurs ta ce a shirye ta ke ta hana dan wasan gaba na Ingila Harry Kane, 29 zuwa wani kulob din Premier a bazara – dai-dai lokacin da Manchester United da Bayern Munich ke zawarcin dan wasan. (90min)
AC Milan za ta ci gaba da nuna sha’awarta ta zawarcin dan wasan Arsenal da Ingila yan kasa da shekara 21 Folarin Balogun wanda a yanzu ya zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a Ligue 1 yayin da yake a matsayin aro a Reims. (Mail)
Milan na zawarcin dan wasan Liverpool mai buga wa Guinea tsakiya Naby Keita, 27. (Mirror)
Liverpool da Newcastle sun gudanar da tattauna wa game da yiwuwar daukan dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Jonathan Tah, 26. (90min)
Manchester United na shirin dauko dan wasan tsakiyar Austria Marcel Sabitzer, mai shekara 28, na din-din-din a bazara idan ya yi rawar gani a lokacin aronsa daga Bayern Munich a Old Trafford. (ESPN)
Tottenham za ta iya zawarcin dan wasan Benfica Rui Pedro Braz idan aka dakatar da daraktan kwallo Fabio Paratici bayan da ake zarginsa a badakalar kudi da ta dabaibaye Juventus. (Mirror)
Dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, 33, zai yi watsi da komawa Los Angeles FC sannan ya yi fafutuka don neman gurbinsa a Chelsea. (Telegraph – subscription required)
Manchester United da Arsenal da Liverpool sun tattauna da wakilin Ansu Fati, 20, mai bugawa Barcelona da Spaniya. (Fabrizio Romano)
Manchester United na sa ido kan dan wasan tsakiyar Belgium, Arthur Vermeeren mai shekara 18. (Mail)
Tsohon dan wasan gaba na Leeds United Jimmy Floyd Hasselbaink na ganin ya kamata kulob din Elland Road ya duba Steven Gerrard a lalubensu na neman sabon koci. (Casinos En Ligne, via Yorkshire Evening Post)