
Asalin hoton, Getty Images
Tottenham Hotspur ta sanya Julian Nagelsmann mai shekara 35 da Bayern Munich ta kora, a jeren mutum na farko da take son ya maye gurbin Antonio Conte, mai shekara 53. (Football Insider)
Spurs na son tattaunawa da Nagelsmann, bayan sanar da ita cewa tsohon kocin na RB Leipzig na da burin komawa kungiyar Firimiya. (Mail)
Sai dai, Nagelsmann na cikin mutanen da Real Madrid ke son ya zame ma ta koci, yayinda da mokomar Carlo Ancelotti ke cikin rashin tabbas. (Sport – in Spanish)
Dan kasar Jamus Thomas Tuchel, mai shekara 49, na son ya dauko mataimakin kocinsa a Chelsea Antony Barry, mai shekara 36 domin su yi aiki tare idan ya tafi Bayern.(Telegraph – subscription required)
Bayern na zakwaɗin naɗa Tuchel saboda fargabar ka da Real Madrid ko Tottenham su dauke shi. (Mirror)
Tuchel zai kuma so ya dauko mai tsaron raga dan kasar Senegal Edouard Mendy, da dan wasan Croatia Mateo Kovacic daga tsohuwar kungiyarsa Chelsea. (Calciomercato, via Football.London)
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta bi sahun abokiyar hamayyarta Manchester City da kuma kulob din Liverpool a zawarcin dan wasan Chelsea Kovacic. (90min)
Barcelona na son saye dan wasan Manchester City Ilkay Gundogan, mai shekara 32. (Athletic – subscription required)
Arsenal za ta sayar da dan wasan da ta kashe kudi wajen sayen sa Nicolas Pepe, ya na zaman aro yanzu haka a Nice. (Sun)
Dan wasan Brazil da West Ham Lucas Paqueta, mai shekara 25, na shirin barin Hammers idan suka fada rukunnin ‘yan dagaji. (Football Insider)
PSV Eindhoven za ta sayar da dan wasan Ivory Coast Ibrahim Sangare, mai shekara 25, Arsenal da Chelsea, Liverpool da Tottenham na zawarcinsa. (90min)
Barcelona na fatan Uefa ba za ta sanya musu haramci kan binciken da take yi musu da bada cin-hanci ba. (Mail)
Mai Chelsea Todd Boehly ya amince a gudanar da wasan tara kudi a Stamford Bridge cikin watan Agusta domin taimakawa Ukraine. (Evening Standard)