Trump da Clinton sun yi muhawara


‘Yan takara a zaben shugabancin Amirka na jam’iyyun Demokrat da Republican wato Hillary Clinton da Donald Trump sun yi muhawararsu ta farko a birnin New York na kasar Amirka.

Yayin muhawarar da suka yi, ‘yan takarar sun yi amfani da zafafaan kalamai wajen zargin junansu da niyar kai kasar Amirka su baro. Hillary Clinton ta nunar da cewar abokin hamayyarta na dogaro a kan wariyar launin fata wajen rarraba kawunan Amirkawa, yayin da Trump ya zargi Clinton ta haddasa rikicin da ake fama da shi yanzu haka a yankin gabas ta tsakiya a lokacin da ta rike mukamin saktariyar harkokin wajen.

Hillary Clinton dai yayin wannan muhawara ta yi alkawarin rage haraji ga masu matsakaicin karfi, shi kuwa Donald Trump baya ga rage haraji, ya yi alkawarin sake tattauna yarjejeniyar kasuwanci. An kiyasta cewar fiye da Amirkawa miliyan 90 ne suka kalli wannan muhawara ta kafar talabijin.

You may also like