Trump; ‘Hillary shaidaniya ce’


Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Repulican Donald Trump ya bayyana abokiyar hamayyarsa ta Democrats Hillary Clinton da shaidaniya, ya yin da yake fama da rikici a cikin jam’iyyarsa.

Da ya ke jawabi a wurin kamfe a Pennsylvania Mista Trump ya zargi sanata Bernie Sanders da marawa Misis Clinton baya.

Mista Trump ya kara da cewa Mista Sanders ya yi yarjejeniya da shaidan, dan kuwa Hillary Shaidaniya ce.

Dukkan jam’iyyun Democrats da Republican dai ciki har da tsohon dan tankarar Republican din John McCain sun yi Allah wadai da kalaman da Mista Trump ya yi amfani da su, ga iyayen wani sojan Amurka musulmi Humayan Khan da aka kashe a kasar Iraqi.

You may also like