Trump: Sai in na yi nasara ne zan amince da sakamakon zabe


trumpTrump: Sai in na yi nasara ne zan amince da sakamakon zabe

Dan takarar shugaban kasar Amurka a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Nuwamba Donald Trump ya bayyana cewa, idan har ya yi nasara a zaben to zai amince da sakamakonsa.

Trump ya yi jawabi a jihar Ohio game da sakamakon zaben shugaban kasar da za a fitar.

A bayanan da Trump suka yi a Les Vegas a makon da ya gabata ya yi zargin ana kokarin yin ba daidai ba game da sakamakon zaben na Amurka, kuma akwai yiwuwar ya ki amincewa da shi.

A wajen taron Ohio Turmp ya fadawa magoya bayansa da cewa, idan har na yi nasara to zan amince da sakamakon wannan babban zabe. Ya kuma sake cewa, Hillary Clinton na shirin lalata sakamakon zaben.

Trump ya ce, sakamako mai kyau kawai zai iya amincewa da shi inda ya kara da cewa, zai iya zuwa kotu don neman hakki game da zaben.

You may also like