Trump ya bawa Najeriya gudunmawar na’urar bentileta 200


Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya cika alkawarin da yayi na bawa Najeriya tallafin na’urar bentileta dake taimakawa marasa lafiya wajen yin numfashi.

Trump a wata tattaunawa da yayi da shugaban kasa Muhammad Buhari cikin watan Afirilu ya yi alkawarin tallafawa Najeriya da na’urorin a yakin da take da cutar Korona.

Amma kuma na’urorin basu samu damar isowa ba sai bayan watanni biyar da yin alkawarin.

Da yake karɓar gudunmawar na’urorin guda 200 daga hukumar USAID a madadin Najeriya ministan lafiya,Osagie Ehanire ya ce kayayyakin kula da lafiya na da matuƙar muhimmanci ga wadanda suke fama da cutar Korona.

You may also like