Trump Ya Bayyana a Karon Farko Tare Da Pence a Matsayin Mataimakinsa


Dan takarar jam’iyyar Republican da ake hasashen shi zata tsayar don yin takarar neman shugabancin Amurka Donald Trump.

 

Ya bayyana yau a karon farko shi da wanda ya zaba a matsayin wanda zai masa mataimakin shugaban kasa idan ya ci zabe.

Inda ya bayyana a birnin New York tare Gwamnan jihar Indiana Mike Pence, ya kuma bayyanawa duniya cewa ga abokin tafita a takarar neman shugabancin Amurka. Trump ya bayyana Pence a matsayin cikakken mutum mai sanin ya kamata.

Haka zalika ya bayyana cewa ya zabe shi ne a matsayin wanda yayi la’akari da shi tun farkon fara takararsa, musamman saboda irin nasarorin da Pence din ya cimma a matsayinsa na gwamnan jihar Indiana.

Ya tabbatarwa da Amurkawa cewa Mista Pence ne zai tsaya kai da fata wajen kare mutuncin Amurkawa da kawo hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ta Republican. A karshe ya dora laifin yamutsin gabas ta tsakiya akan gwamnatin Obama.

You may also like