Trump ya ce za a yi magudi a zaben Amirka


 

 

Dan takarar jam’iyyar Republican a zaben shugaban Amirka Donald Trump ya ce kafafen watsa labarai a Amirka na kokarin bada gudumawarsu wajen murde zabe shugaban kasa don Hillary Clinton ta samu nasara.

19558261_303-1

Trump na wadannan kalamai ne lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa a New Hampshire a wani bangare na cigaba da yakin neman zabe. Dan takarar na jam’#yyar ta Republican ya ce tun ma ba a kai ga yin zaben ba kafafen watsa labarai na kasar sun rigaya sun murde shi inda suke yada karairayi game da shi da zantukan da ba su da tushe a wani yunkuri na ganin sun dora Hillary kan gadon mulki. A dan tsakanin nan Mr. Trump na shan suka daga abokan hamayya da ‘yan kasar kan batun cin zarafin wasu mata ake zargin ya yi a shekarun da suka gabata, zargin da Trump din ya musanta.

You may also like