Trump ya sanya hannu kan takardun hana ‘yan gudun hijira shiga Amurka


 

 

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan takardun umarnin da ya bayar na hana ‘yan gudun hijira shiga Amurka.

Umarnin na Trump da aka sam fitar sa ga jama’a na cewa, daga yanzu babu wani dan kasar Siriya da zai shiga Amurka har sai abin da hali ya yi.

A cikin kwanaki 120 kuma babu wani dan gudun hijira daga wata kasa da zai shiga Amurka.

Bayan wannan lokaci kuma, Hukumar Leken Asiri ta Amurka da ma’aikatun harkokin cikin gida da na waje ne kadai za su bayar da shawara game da daga wacce kasa za a iya karbar ‘yan gudun hijira.

A yanzu kuma nan da kwanaki 30 ‘yan kasashen Iraki, Libiya, Siriya, Iran, Sudan, Somaliya da Yaman ba za su shiga Amurka ba ko da wacce irin Visa suka je.

Fadar White House za ta bayar da cikakken bayani game da wannan kudiri.

You may also like