Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin samar da zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasdinawa
Trump ya bayyana haka a yayin ganawarsa da shugaban al’ummar Falasdinu Mahmud Abbas a yankin yamma ga kogin Jordan a wannan Talata.
Trump zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasdinawa.