Trump ya zama dan takarar Republican


 

Jam’iyyar Republican a kasar Amurka ta tabbatar wa Donald Trump takarar shugabancin Amurka a zaben da za’ayi a watan Nuwamba.

Bayan an dauki dogon lokaci ana yakin neman zabe, Trump ya kada mutane 16 da suka shiga takarar wajen samun nasara.

A jawabin da ya yiwa dubban magoya bayan sa da suka taru a Cleveland, Trump ya ce zasu samu nasara, kuma su sake kwace kasar su.

Mista Trump ya ce shugabancin su zai kasance mai sanya Amurkawa a sahun farko, inda za su sake gina rundunan sojojin kasar da kuma kula da tsoffin sojojin, kana za kuma su karfafa tsaro a iyakokin Amurka da murkushe ISIS.

A karshe ya kuma bayyana burinsa na mayar da doka da oda, wanda ya ce ya zama wajibi a kan gwamnatinsu muddin sukayi Nasara.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like