Zababben shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya zargi shugaban kasar mai barin gado Barack Obama, da kawo tarnaki a shirye-shiryen mika masa mulkin Amurka.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, a jiya Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, Obama yana son ya kawo matsala ga shirin mika masa mulki a ranar 20 ga watan Janairu mai kamawa, amma bai yi karin bayani kan irin matsalolin da yake zargin Obama da haifarwa kan wannan batu ba.
Daga bisani bayan yada wannan labari, ‘yan jarida sun tambaye shi kan abin da yake nufi, amma ya yi mirsisi kan batu, inda ya nuna cewa suna tattaunawa da Obama ta wayar tarho, kuma za a warware komai ta hanyar lumana.
A bangare guda kuma Trump ya soki lamirin Obama da cewa ya mayar da Isra’ila saniyar ware, amma hakan zai kawo karshe da zaran ya karbi mulki, kuma lamurra za su canja a majalisar dinkin duniya kan kyamar da ake nuna wa Isra’ila.