Trump yayi amai ya lashe


 

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam’iyyar Republican Donald Trump yayi amai ya lashe, inda yace batun zargin da ya yiwa Shugaba Barack Obama da Hillary Clinton na kafa kungiyar IS da wasa yake.

Kamar dai yadda ya saba, Donald Trump ya zargi kafafen yada labarai da yiwa kalamansa gurguwar fahimta, inda yace sun rawaito ba dai-dai ba.

A lokacin gangamin yakin neman zaben sa a Florida ne Trump ya Ambato sunayen Obama da Hillary dake takara a Democrat a matsayin masu taimakawa IS, tare da sake maimata hakan a wata hirar da yayi jiya alhamis.

You may also like