Ana sa ran a Larabar nan Shugaba Donald Trump zai sanya hannu kan wasu dokoki da za su iya hana baki da Musulmai shiga Amurka a ‘yan kwanakin da ke tafe.
Kafafen yada labaran Amurka sun rawaito cewa zai sa hannu tare da yin dokar tsaurara matakan tsaro a iyakar kasar da Mexico, a ziyarar da zai kai ma’aikatar tsaron cikin gida a ranar Laraba.
Ya na kuma son ganin an tsaurara matakai ga masu neman shiga kasar, da suka fito daga kasashe 7 na yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kasashen Afurka da Musulmai suka fi yawa.
Samar da sauye-sauye a fannin shige da fice na Amurka shi ne babban batun yakin neman zaben Donald Trump.
A lokacin yakin neman zabensa ya lashi takobin gina katanga tsakanin Mexico da Amurkar domin hana shigar bakin haure kasar tasa.
Sannan kuma da haramta wa Musulmai zuwa Amurka, a matsayin wani mataki na yaki da ta’addanci, manufar da daga baya ya yi mata kwaskwarima da cewa ta yaki da tsattsauran ra’ayi ce.
A bisa tsarin mulkin Amurka dai , an haramta nuna wariya kan addinin mutum, amma ana ganin a karkashin mulkin Trump, zai kawo damar nuna wariyar karkashin matakan gaggawa na yaki da barazanar ta’addanci.
Sai dai ana ganin matakin zai iya harzuka kungiyoyin agaji da masu kare hakkin ‘yan ci-rani, idan aka yi la’akari da halin da ‘yan gudun hijirar Syria ke ciki wanda ke kara munana.