Tsananin Sanyi Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 50 A Yankin Turai Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon tsananin sanyi a kasashen Turai cikin kwananki biyu da suka gabata.
A cewar hukumomin kasashen da abin ya shafa akasarin wadanda suke mutuwa marasa muhali ne da bakin haure, yayin da sanyi tattare da dusar kankara ke sake tsananta.
Kasashen Rasha da Poland da Italy da Bulgaria ne aka fi samun asaran rayuka, daga watan Nuwamba zuwa yanzu sama da mutane 50 sun kwanta da dama a sassan Turai.

You may also like