Yan sandan masu kula da bangaren damfara na musanman(SFU) jiya sun gurfanar da maza ukun ne a baban kotun kasa Legas akan sayan wayar i-Phones har tsawon naira millian talatin da biyar(N35m) daga kamfanin cinikaiya yanar gizo-gizo konga,ba tare da sun biya su ba.
A na tuhumar John Nweke,Stephen Anike da Kelech Emenike akan bawa Konga cheque in banki bayan babu kudi a cikin asusun nasu kuma yan sandan na tuhumarsu da karban wayoyin hanun bayan suna da masaniyar cewa yin haka satace kuma damfara ce.amman duk kansu basu amsa laifinsu ba.