Tsarin EU na bai wa sojojin Nijar horo | Labarai | DWAna dai ganin rikicin kasar Mali da ke makwabtaka, ka iya tsallakawa zuwa Jamhuriyar ta Nijar. ‘Yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayin addini na ci gaba da kame yankunan Malin, tun bayan ficewar uwar gijiyarta da ta yi mata mulkin mallaka Faransa daga kasar. Cikin watan Disambar bara ne kungiyar ta Tarayyar Turai ta yanke shawarar kaddamar da tasarin bai wa sojoji horo na shekaru uku a Jamhuriyar ta Nijar da ke zaman guda cikin kasashe matalauta a duniya, inda za ta jibge dakarun kungiyar 50 zuwa 100 domin bayar da horo a fannoni dabam-dabam. Ana sa ran Jamus da tun a shekara ta 2018 ne sojojinta 150 ke bai wa takwarorinsu na Nijar din horo kafin ta kawo karshen tsarin a shekarar da ta gabata ta 2022, za ta aike da tawagar sojojinta kimanin 60. Har kawo yanzu dai akwai kimanin sojojin Jamus dubu daya da 100 a Mali, kuma mafi yawansu na garin Gao ne da ke yankin arewacin kasar.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like