Tsarin takardu shedda na mallakar gidaje a Filato


 

 

 

A Najeriya gwamnatin Jihar Filato ta bullo da sabon tsari wajen mallakar sheddar gidajen zama da kuma sheddar mallakar filaye.

To da wannan sabon tsari dai dukkan masu sheddar fili ko takardun gida gwamnatin ta Filato ta ce za ta karbesu,to sai dai kuma jama’a sun mayar da martani a game da wannan sabon tsari, domin kuwa yayin da wasu masu gidajen zama ke maraba,wasu kuma na yin dari-dari.

A wata ganawa da gidan radiyon DW ya yi da kwamishinan filaye na jihar Filato Barrister Festus Fuanter, ya bayyana cewar za su samar wa jama’a takardun ne kan kudi kalilan sakamakon halin rashin kudi da ake fama da shi.Binciken na nuna cewar a can baya ba kasafai jama’a kan sami irin wannan sheddar gidaje ba, sakamakon irin jan kafa da ma dawainiyyar da jama’a kan yi kafin su sami takardun shedan. Don haka nema wasu lokutan a kan fuskanci rigingimu tsakanin al’umma game da filaye.Babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa na jihar Filato Bulus Dabit, ya ce suna kan himmar fadikar da jama’a mahimmancin da ke tattare da wannan sabon tsari.Masu anazarin al’amura dai sun kawo shawarar cewar yakamata gwamnatin ta Filato ta tabbatar cewar takardu da za ta karba daga jama’a, masu shi ne na hasali, don gujewa hada wata rigimar tsakanin jama’ar da tun hasali suna rikici kan fili ko gida.

You may also like