An tsaurara kaiwa Daesh hari a Libiya


 

 

 

An tsaurara kai hare-hare kan ‘yan ta’addar Daesh wanda hakan ya janyo arangama tsakaninsu da jami’an tsaron kasar Libiya.

Dakaru da ke da alaka da gwamnatin hadin kan kas ata Libiya sun kwace iko da wata unguwa da ke arewacin birnin Sirte.

An kori ‘yan ta’addar daga unguwa ta uku inda aka kuma dinga harba musu bama-bamai tare da rushe gine-ginen da suke zama a ciki.

Ana ci gaba da rangamar inda aka kashe dakarun gwamnati 5 tare da jikkata wasu 17.

You may also like