Majalisar wakilai ta yanke shawarar bincikar Abdulmuminu Jibrin da kuma Muhammad Gudaji Kazaure, kan furucin da su kayi na cewar majalisar na shirin tsige shugaban kasa Muhammad Buhari.
Ya yin da Jibrin ya ce zaman hadin gwiwa gaggawa na sirri da zauren majalisun suka gudanar batu ne na ya’yan jam’iyyar PDP, Kazaure ya zargi wasu yan majalisar da tattara sa hannun neman tsige shugaba Buhari.
Kazaure ya bayyana sunayen, Ossai Nicholas Ossai na jam’iyar PDP daga jihar Delta da kuma Kingsley Chinda daga jihar Rivers a matsayin wadanda suka rattaba hannu a takardun tsige shugaban.
Yan majalisar biyu sune suka daga batun a zaman zauren majalisar na ranar Laraba inda suka ce hakan ya shafi damar da suke da ita.
A karshe zauren majalisar ya mika batun ga kwamitin d’a’a na majalisar.