Tsoffin Ministocin Johnathan 11 Na shirin Barin PDP Zuwa APC Akwai kwararan hujjoji cewa tsoffin Ministocin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan za su sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC. Bincike ya nuna tsohon Gwamna Jolly Nyame, Sanata Andy Uba da wasu Sanatocin Jam’iyyar PDP na fuskantar matsin lamba akan su koma Jam’iyyar APC. 
Wasu daga cikin ministocin da ake bincike sun hada da Nurudeen Mohammed; Sanata Musiliu Obanikoro; Bashir Yuguda; tsohon ministan lantarki, Mohammed Wakil; Bala Mohammed; Diezani Alison-Madueke; Oloye Jumoke Akinjide; Ambasada Aminu Wali;  Farfesa Viola Onwuliri; tsohuwar Minista Nenadi Usman; Sanata Joel Ikenya da Femi Fani-Kayode. Ibrahim Shekarau da Musa Muhammad Sada; da kuma Asabe Asmau Ahmed.
Sauya shekar tsohon ministan sufuri Umar Idris, daga PDP zuwa APC a makon da ya gabata kamar sharar hanya ce ga tsoffin Ministocin.

You may also like