Tsoffin Shugabannin Nijeriya Na Bin Buhari Albashin Watanni 10


 

Gwamnatin tarayya a jiya Alhamis ta bayyana cewa an shafe watanni 10 cir ba ta biya tsoffin shugabannin Nijeriya kudaden albashinsu da alawus alawus din su ba a sakamakon matsin tattalin arziki.

Sakataren gwamnatin tarayya, Babachair Lawan shi ya bayyana haka ga tawagar kwamitin majalisar dattawa masu lura da yadda ma’aikatun gwamnati ke aiki, a karkashin shugabancin Sanata Tijjani Kaura (APC, Arewacin Zamfara) a lokacin da suka ziyarci ofishin sa.

Babachir ya fadi cewa wannan al’amari ya shafi har Alhaji Shehu Shagari wanda ya ke tsoho dan shekaru 90 a yanzu.

Sauran sun hada da Olusegun Obasanjo; Goodluck Jonathan; janaral Ibrahim Babangida mai ritaya; janaral Abdulsalami Abubakar; janaral Yakubu Gowon da Chief Ernest Shonekan.

You may also like