
Tsohon dan wasan Ingila da aka lashe Gasar Kofin Duniya da shi George Cohen ya mutu.
Tsohuwar kungiyarsa Fulham ce ta wallafa labarin mutuwar mai tsaron bayan nata, kuma ya cika ne yana da shekaru 82.
Marigayin na daga cikin tawagar da ta lashe kofin duniya a Wembley a 1966, kuma shi ne ma mataimakin kyaftin a wasan karshe da suka doke Jamus ta Yamma 4-2.
George Cohen ya kammala ilahirin rayuwarsa ta kwallon kafa a Fulham, kuma ya buga wa Ingila wasanni 37.
A 2016 ne kungiyar ta London ta kafa butum-butuminsa a gaban filinta na Craven Cottage, kuma a 1998 ne ta sayi sarkarsa ta zinari da suka lashe a 1966, kan fam 80,000.
Abokan wasansa da suka rage Sir Bobby Charlton da Sir Geoff Hurst, duka sun wallafa sakon ta’aziyya ga iyalan Cohen.