
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan AC Milan da Bologna Sinisa Mihajlovic ya mutu yana da shekaru 53.
Tsohon mai tsaron bayan na tsohuwar Yugoslavia wanda ya taba lashe kofin zakarun Turai a 1991, ya yi jinyar kansar jini da ya sanar ya kamu da ita tun 2019.
An kuma yi masa tiyata a lokacin kuma ya warke. To amma daga baya aka sake masa gwaji aka tabbatar masa cewa cutar ta dawo.
Mihajlovic ya taba cin kofin gasar Serie A ta Italiya da Lazio da Inter Milan, kuma ya buga wa Roma da Sampdoria wasanni.
A matakin kasa Mihajlovic ya buga wasanni 63 tsakanin 1991 zuwa 2003.
Hakama ya wakilci tsohuwar Yugoslavia a gasar cin kofin duniya ta 1998, da kuma ta nahiyar Turai a 2000.
Bayan ritayarsa, Mihajlovic ya horar da tawagar kasarsa da kuma tsohuwar kungiyarsa Bologna ta Italiya, har zuwa watan Satumba da aka sallame shi saboda gaza samun nasarori.
Hukumomin kwallon kafa na Serbia da kuma Serie A duka sun fitar da sanarwar alhinin rashin Sinisa Mihajlovic, inda hukumar ta Serbia ta ce ”duniyar kwallo ta yi rashin shahararren dan wasa wanda makura ne a bugun tazara a tarihin kwallon kafa.”
Ta kara da cewa ” ya bar tabon da ba zai taba gushewa ba ga Serbia da gasar Serie A.”