
Asalin hoton, Getty Images
Vialli yana matsayin dan wasa kuma koci lokaci da Chelsea ta lashe European Cup a 1998
Vialli ya yi ta fama da kansar hanji tun 2017 da aka yi masa aiki a kanta, kuma an sake yi masa aiki a kanta a 2021.
Ya sanar da tafiya hutu na wani dan lokaci a aikin da yake yi da tawagar Italiya a watan Disamba domin mayar da hankali kan lafiyarsa.
“Gianluca mutum ne da ake matukar kauna, kuma ya bar wani gibi da ba za a iya cike wa ba,” in ji shugaban hukumar kwallon kafa ta Italiya Gabriele Gravina.
“Mutum ne da zai iya duk wani aiki da aka ba shi, labarin rasuwarsa ya kada mu”.
Hukumar kwallon kafar Italiya ta tabbatar da za a yi shiru na minti Daya a duk wasannin wannan makon, domin girmamawa ga marrigayi Vialli.
Vialli wanda y afara buguwa Italiya wasa a 1985, kafin ya rasu ya buga mata wasa 59.
A 1984 ne ya koma Sampdoria inda ya ci kofin Serie A da Europian Cup, kuma ya shafe shekara takwas da kungiyar.
Cikin wata sanarwa da Sampdorian ta fitar tace: “Ba zamu taba mantawa da kwallaye 141 da ya ci ba, salon wasansa da soyayyarsa da kulob dinmu ba.”
Vialli ya taimaka wa Sampdoria ta kai wasan karshe na gasar nahiyar Turai a 1992, bayan rashin nasrar kuma da ta yi a hannun Ajax, dan wasan ya koma Juventus kan kudi da suka kai fan miliyan 12 wanda a wancan lokacin shi ne mafi tsada.
Vialli ya yi kaka hudu tare da Juventus ya kuma lashe gasar zakarun turai da Uefa da kuma Serie A.
Itama Juventus ta mika ta’aziyyarta ga iyalan dan wasan, wanda har zuwa ranarsa ta karshe yana kaunar kungiyar.
Vialli ya koma Chelsea a 1996 ba tare da eja ba, a 1998 kuma ya zama dan wasa kuma koci a karon farko da dan kasar Italiya ya zama mai horaswa a Premier, wanda ya maye gurbin Ruud Gullit a karshen kaka, Vialli ya kai Chelsea ga nasara a kofin Lig da Uefa da Super Cup.
Ya kuma daukarwa Chelsea kofin FA a 2000 da Charity amma na kore shi a kakar saboda rashin kokari a farkon kaka.