
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon Fafaroma na 16 ya mutu a gidansa da ke fadar Vatican inda yake zaune tun bayan da ya yi murabus kusan shekaru 10 da suka gabata.
Marigayi Fafaroma ya mutu yan da shekara 95 a duniya.
An haifi Joseph Ratzinger a Jamus, an zabe shi ya jagoranci Cocin Roman Katolica a 2005, bayan mutuwar John Paul na biyu.
Shekara takwas bayan nan, y zama Fafaroma na farko da ya sauka daga karagarsa cikin shekara 600, yana cewa ba shi da karfin gudanar da ayyukansa.
A yayin shugabancinsa, Cocin ta fara fito-na-fito da cin zarafi ta fuskar lalata da malaman coci ke yi a fadin duniya.