Tsohon Ministan Abuja zai damkawa gwamnatin tarayya kadarori 14


Babbar kotun tarayya dake Abuja, ta amince da bukatar Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, kan kwace gidaje da kadarori 14 mallakin tsohon ministan Abuja, Bala Muhammad.

A watan Satumba hukumar EFCC ta kwace kadarorin.

Tsohon ministan na fuskantar shari’a da kan  yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka, saba ka idar aikin ofis da kuma zambar kudi miliyan ₦864.

Mai shari’a Nmandi Dimgba, alkalin dake shari’ar yayi umarnin a damkawa gwamnatin tarayya kadarorin cikin kwanaki 21.

Tun farko lauyan hukumar EFCC, Ben Ikani, ya shaidawa kotun cewa ana zargin tsohon ministan ya mallaki gidajen ne ta hanyar kudaden haram.

Ikani yace duk wani dake da sha’awa shiga shari’ar ko kuma yake jin bai dace ba gwamnati ta karbi kadarorin to ya zo ya bayyana hujjojinsa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like