Tsohon shugaban Jamus Walter Scheel ya rasu. Fadar shugaban kasa Joachim Gauck ita ta fitar da wannan sako a ranar Laraban nan, inda ta ce tsohon shugaban kasar ya rasu bayan lokaci mai tsawo na rashin lafiya.Walter Scheel tsohon shugaba a Jamus. 

Tsohon shugaban kasar Jamus Walter Scheel da ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita Yammaci da Gabashin Jamus ya rasu yana da shekaru 97.Fadar shugaban kasa Joachim Gauck ita ta fitar da wannan sako a ranar Laraban nan, inda ta ce tsohon shugaban kasar ya rasu bayan lokaci mai tsawo na rashin lafiya.Shi dai tsohon Shugaba Scheel ya kasance mai ra’ayi na ganin hadin kan Turai ta tabbata. An haife shi a ranar takwas ga watan Yuli shekarar 1919 birnin Solingen, da ke aYammaci na Jamus.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like