Tsohon shugaban kasar Isra’ila Shimon Peres ya rasu


 

 

 

 

Shugabanin Kasashen duniya sun fara tofa albarkacin bakin su dangane da rasuwar tsohon shugaban kasar Isra’ila Shimon Peres, wanda ya rasu yau laraba yana da shekaru 93.

 

 

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana Shimon Perez a matsayin abokin da ya kasa kaucewa manufar sa ta zaman lafiya, yayin da Bill Clinton da George W. Bush da dan sa George Bush tsoffin shugabanin kasar suka bayyana shi a matsayin gwarzo.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana marigayi Perez a matsayin mai san zaman lafiya.

Shimon Peres, wanda ya rike mukamin Firaministan Isra’ila sau biyu da shugaban kasa sau guda, ya kuma jagoranci tattaunawar zaman lafiya da Falasdinawa, ya rasu yana da shekaru 93 sakamakon bugun zuciyar da ya samu ranar 13 ga watan Satumba, inda aka kwantar da shi a asibitin Tel Aviv.

An haife shi ne ranar 12 ga watan Agusta na shekarar 1923 a Vishneva dake kasar Poland a wancan lokaci kafin yayi kaura zuwa Falasdinu a shekarar 1934 yana da shekaru 11.

An zabe shi Dan Majalisa a shekarar 1959, ya kuma zama Firaminista tsakanin shekarar 1984 zuwa 1986 a karkashin gwamnatin hadin kai.

A shekarar 1993 ya jagoranci tattaunawar zaman lafiyar da akayi a asirce da kungiyar Falasdinu wanda ya kai ga samun yarjejeniyar Oslo.

A shekarar 1994 an bashi kyautar Nobel tare da Yitzhak Rabin da da kuma Yaseer Arafat, shugaban Falasdinawa saboda rawar da suka taka na samun zaman lafiya.

Peres ya gaji Rabin a matsayin Firaminista a shekarar 1995 bayan an kashe shi ranar 4 ga watan Nuwamba.

An zabe shi shugaban kasar Israila na 9 a watan Yuni na shekarar 2007, ya kuma sauka daga mukamin a watan Yuli na shekarar 2014 gaf da cika shekaru 91 a duniya, ya kuma rasu yau da safe.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like