Tsohon Shugaban Kwastam Ya Mayar wa da Gwamnatin Tarayya N1bn


 

Tsohon kwamftrolla janaral na hukumar hana fasa kauri a Nijeriya, Alhaji Abdullahi Dikko, ya mayar da naira biliyan daya ga gwamnatin tarayya a cikin kudaden da ake zargin ya sata yayin da yake kan mukamin sa.

Wannan al’amari ya zo a daidai lokacin da tsohon karamin ministan tsaro Musiliu Obanikoro shi ma ya mayar da Naira miliyan 100 ga hukumar EFCC.

janaral din wanda ya rike mukamin a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2015 ya shiga hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ne bayan da aka zarge shi da yin hafzi da makudan kudade da adadinsu ya kai N40bn daga lalitar hukumar ta kwastam.

Bayan da aka tsare shi ne, hukumar ta sake shi a sakamakon tabarbarewar lafiyar sa. Daga bisani ya yarda cewa zai biya kudaden a hankali.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka ya mayarda naira biliyan daya da kuma wata naira miliyan hudu.

Tuni EFCC ta kwace wani gidansa guda daya da farashinsa ya kai naira biliyan biyu.

Hukumar na ci gaba da sanya masa ido yayin da ya maido da sauran kudaden.

You may also like