Tsohuwa Mafi Yawan Shekaru A Duniya Ta Cika Shekaru 117Emma Morano, itace tsohuwar da tafi tsawon rai a fadin duniya, tsohuwar mai shekaru dari da goma sha bakwai 117, ta yi bukin cikar ta shekarun, da bayyanar da cewar tana da sauran karfinta. Ta hure wutar kyandiran dake saman kek din da aka yi mata lokacin bukin. Tsohuwar ‘yar asalin garin Verbania a kasar Italiya ce.
Shugaban kasar Italy, Mr. Sergio Mattarella, ya aika mata da katin murna, kuma ya bayyana a gidan talabijin na fadar shugaban, don taya ta murna da fatar Allah ya bata tsawon kwanaki da lafiya masu albarka.
An ba ta nau’in abinci da tafi sha’awa, a rayuwar ta da madara a yayin bukin. Lokacin bukin, ta gayama mutanen da suka halarci bukin cewar, ba dai zasu sata yanka kek din ba dai? sai ta kara da cewar, gaskiya naji dadi matuka da Allah ya nuna mun wannan ranar da na cika wadannan shekarun.
Awowi kadan bayan bukin sai ga wani kek, daga shugaban karamar hukumar garin da take. Ya kawo mata don karrama ta, inda yayi jawabin cewar, Morano, itace daya tilo da ta rage a cikin mutanen zamanin ta daga shekarun 1880.

You may also like