Uwargida Marry Ebikake, tsohuwar kwamishinar sufuri ta jihar Bayelsa da wasu yan bindiga suka sace rana ɗaya tare da wani soja a wurare daban-daban dake jihar Bayelsa ta samu yancinta.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa an sako Ebikake da ƙarfe 3 na daren ranar Juma’a amma har yanzu ba’a san halin da sojan ke ciki ba.
Mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar Bayelsa, DSP Asinim Butswat ya tabbatarwa da NAN haka ranar Juma’a, a Yenagoa.
Amma kuma Butswat yace bashi da cikakken bayani kan yadda aka sako ta.
“Ina tabbatar da cewa tsohuwar kwamishinar an sake ta kuma ta koma wajen iyalinta amma bani da cikakken bayani,” yace .
Ebikake an yi garkuwa da ita a gidanta dake yankin Igbogene na ƙaramar hukumar Yenagoa dake jihar.
Sojan wasu yan fashin teku ne suka yi garkuwa da shi a mashigar ruwa dake yankin Foropa da Azuzuama a ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu dake jihar.
Sojan da aka bayyana da suna Rotimi na cikin jirgin ruwa akan hanyarsa ta zuwa Yenagoa lokacin da aka yi garkuwa da shi yayin da aka harbe matukin jirgin.