Tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Ta Koma Gidan Haya A Birnin London 


Diezani Alison Madueke tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya, yanzu dai duniya ta fara juya mata baya, matar da abaya ta gwala-gwalai, lu’u-lu’u, makudan kudade da kuma manyan gidaya ciki da wajen Najeriya yanzu duk wannan dukiya na nema ta zama tarihi.

Jaridar The Cable ta lura cewa yayin da kadarorinta dake Birtaniya da darajarsu takai fam miliyan   £11, ake nema  a aiyana su a matsayin dukiya da aka mallaka da kudaden haram kuma ake shirin kwace su, yanzu dai bata da wani zabi, illa ta rage irin rayuwar jin dadin da ta saba yi a baya.

 Yanzu dai tsohuwar ministar ta fice daga gidan da take inda ta kama hayar wani gida cikin wani rukunin gidaje inda a baya take da gida wanda abokan kasuwancinta Jide Omokore, da Kola Aluko suka saya mata kan kudi dala miliyan $2.

Tuni dai Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta EFCC ta rufe duk wani asusun banki mallakar tsohuwar ministar da kuma duk wani mutum da yake da kusanci da ita.Hakan na nufin tsohuwar ministar bata da kudade kamar yadda take dasu a baya.  

  

 

You may also like