Tsohuwar Shugabar kasar Liberia ta lashe kyautar shugabanci ta Mo Ibrahim 


Ellen Johnson Sirleaf, tsohuwar shugabar ƙasar Liberia ta lashe kyautar Mo Ibrahim  da ake bawa Shugabannin Afirka da suka nuna ƙwazo lokacin da suke kan mulki kuma suka bar mulki ya yin da wa’adinsu ya ƙare.

Ita ce shugaba mace ta farko da ta taɓa lashe gasar.

Sirleaf wacce ta taɓa lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2011 ta zama shugabar kasa a shekarar 2006 an kuma sake zaɓarta karo na biyu a shekarar 2011.

“Ellen Johnson Sirleaf ta karɓi ragamar mulkin Liberia lokacin da aka lalata ƙasar ga baki ɗaya bayan kammala yaƙin basasa ta kuma jagoranci shirin sasantawa da ya mayar da hankali kan gina ƙasa da kuma ginshiƙan dimakwaradiyarta,” a cewar Salim Ahmed Salim shugaban kwamitin bada kyautar.

Mutumin da ya kirkiro da kyautar shahararren attajirin nan dan asalin kasar Sudan mazaunin Birtaniya, Mo Ibrahim ,ya ce ya yi farin ciki da Sirleaf ta kasance mace ta farko da ta lashe kyautar.

Sirleaf ta bar mulki a shekarar 2017 inda tsohon zakaran ƙwallon ƙafa na duniya, George Weah ya gaje ta a matsayin sabon shugaban ƙasar.

Waɗanda suka lashe kyautar za su karɓi kuɗi dalar Amurka miliyan $5 a tsawon shekaru 10 da kuma dala $200,000 duk shekara har ƙarshen rayuwarsu.

You may also like