Tsokaci Kashi Na Daya: Wai Shin Meyasa Garkuwa Da Mutane Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya? Garkuwa da mutane dai wata dabi’a ce da yan Najeriya suka dauka yanzu, ko kuma ince wani nau’in kasuwanci ne, tunda idan sunyi suna samun nasara a mafi yawanci lokuta.

Meyasa yan Najeriya suke garkuwa da mutane? 

Mafi yawanci mutane zasu iya amsa wannan tambayar da cewa rashin aikin yi ne da bakin talauci yake jawo hakan. Amma ni a gani na, ba haka bane yake jawo ba, masu garkuwa da mutane basa taba kama talaka da niyyar a biyasu diyya, sai dai su sami wani hamshakin mai kudi, ko dan gidan hamshakin mai kudi,’ya’ yan gidan sarauta, ‘yan siyasa, masu rike da manyan mukaman gwamnati,’ yan majalissu, sanatoci, ‘ya’ yansu, ko matansu. 

Shin me yasa basa kama talaka? Saboda bazasu samu ko sisi ba. Amma a tunanin dukkan dan Najeriya a yanzu, duk wani dan siyasa kawai barawon gwamnati ne, duk wani mai kudi toh baya taimakon talakawa, duk wani mai mulki toh yana danne hakkin na kasa dashi. 

Masu garkuwa da mutane suna amfani da wannan ne, wajen ganin ai kudin da za’a basu kamar kudin gwamnati ne, kuma kudin gwamnati nasu ne wands kuma abin ba haka yake ba. Ba’ayi gwamnati dan ta rabawa jama’a kudi ba, anyi gwamnati ne don tabbatar da doka da oda a cikin al’umma, yiwa al’umma ayyuka  raya kasa, bawa al’umma ilimi da tsaron lafiyar su. 

Bincike ya nuna cewa, sama da kaso 80 cikin dari na masu garkuwa da mutane matasa ne wadanda shekarunsu basufi 25 – 40 ba. Shin meyasa matasan Najeriya suke dogaro da sai an dauko an basu? Shin meyasa zuciyoyin matasan Najeriya suke karkata wani bangare maras kyau? Shin meyasa matasan Najeriya basa amfanin da kwakwalwar su wajen kirkirar abu mai amfani wanda bama su ba, ahalinsu zasu amfana dashi. Shin meyasa matasan Najeriya suka zama kasallu kuma suke dauka cewa kudi a sauqi ake samunsu? 

Rashin amsar wadannan tambayoyi shine babbar silar da yake jefa matasa cikin munanan halaye, fashi da makami, yada farfaganda da a tada zaune tsaye, garkuwa da mutane, Shaye-Shayen miyagun kwayoyi, rashin zuwa makaranta, fadace fadacen daba da sauransu. 

Hausawa suna cewa, maraina kadan, toh fa lallai barawo ne. Akwai kananan sana’o’i da mutum zaiyi ya rufawa kansa asiri har da iyalansa, amma matasa basu da hakuri, komai sana’a rainon ta ake kamar yadda ake rainon jariri, ba wai a dare daya ake cin gajiyar ta ba, a hankali in mutum ya fara, sai kaga Allah ya sa masa albarka ya daukaka shi. 

Dole mu matasa sai mu cire zukatan mu daga cewa lallai sai gwamnati ta taimaka mana, dole ne mu taimaki kanmu kafin taimakon gwamnati yazo garemu, dan abu ne marar yiwuwa ace gwamnati ta taimakawa kowa lokaci guda. Zukatan matasa duk a mace suke, yanzu in ka duba zuciyar wani, zakaga cewa cike yake burirrika wanda shi kansa yasan in bai tashi ya nema ba, toh abu ne mai wahala ya samu cikar burinsa. 

Matasa dole su daina raina sana’a, gwamnati dole ta tallafawa matasa masu kananan sana’o’i domin su bunkasa suma su kafa wasu. 

Zamu ci gaba da wannan rahoto in sha Allahu… Meyasa garkuwa da mutane ya zama ruwan dare?

You may also like