Tsugune bata kare ma Hillary Clinton ba


 

Ga dukkanin alamu tsugune bata kare ma Hillary Clinton ba,domin amfani da akwatin imel dinta da ta yi a wajen tara sirrukan kasa a lokacin da ta rike mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka, na shirin zama katanga tsakanin ta da karagar mulki.

Kamar yadda jadawlin zaben kasar Amurka ya nuna,Amurkawa zasu jefa kuri’a nan da kwanaki 11 masu zuwa.

Hukumar leken asiri ta kasar Amurka FBI ta ce zasu sake gudanar da bincike kan batun akwatin İmel.
Shugaban FBI James Comey, ya ce wannan sabon binciken ya sha bamban da wadanda aka yi a baya,domin a wannan karon an samu karin dalilai wadanda ke da alaka da kasar Amurka a  akwatin imel din Hillary Clinton.

Comey ya kara da cewa,ko a baya ma yin kacibus da bayanan da suka jibanci kasar Amurka da suka yi a cikin akwatin imel din Hillary ne yasa suka fara bincike a kanta.

Haka zalika ya ce babu makawa ‘yar takarar Demokrat ta taka doka,amma ba za’a ce ta yi da gangan ba.

Duba da akalumma da aka fitar a baya bayan nan,Hillary Clinton ta shige gaban Donald Trump da maki 5.

Amma labarin akwatin imel ya haifar da gushewar yarda a tsakaninta da magoya bayanta.

A gefe daya kuma, da yake jawabi a wani taron siyasa,dan takarar Republicains Trump ya ce kamata ya yi a sake ingiza keyar wacce ta aikata babban laifi kana ta haifar da barazana ga tsaron Amurka gaban kotu.

Hillary Clinton ta nemi yafiya ga daukacin al’umar kasarta game laifin da ta aikata.

You may also like