Tsvangirai jagoran ƴan adawar Zimbabwe ya mutu


Morgan Tsvangirai shugaban jam’iyar MDC me adawa a Zimbabwe ya mutu.

Dan siyasar wanda yake fama da cutar sankara ya mutu a ƙasar Afrika ta Kudu ranar Laraba.

“Zan iya tabbatar da cewa ya mutu da yammacin yau, iyalinsa su suka sanar dani haka,” Elias Mudzuri mataimakin shugaban jam’iyar ta MDC ya shedawa manema labarai haka.

Tsvangirai wanda yake fama da cutar sankarar hanji ya dade yana jiya a wani asibiti dake ƙasar Afrika ta Kudu.
Yana kwance asibitin lokacin da shugaba Robert Mugabe ya miƙa mulki.Tsvangirai dole ya katse tafiyar tasa inda ya dawo gida domin sheda bikin miƙa mulki kasarsa.

A baya dai ya kasance na hannun daman shugaba Mugabe kafin su raba gari inda ya zama babban mai adawa da shugaban.

An haife shi a shekarar 1952 a ƙauyen Buhera dake da tazarar kilomita 200 kudu  da Harare babban birnin ƙasar.

You may also like